“Idan ruwan dagwalon nukiliya ba shi da illa, har ma za a iya shan sa kamar yadda muka ji ta bakin ‘yan siyasar kasar Japan, to me ya hana su sha, ko su ajiye shi har tsawon shekaru 100 nan gaba?” Wannan dai tambaya ce da wani dan kasar Japan ya yi a ran 11 ga watan nan, yayin da ya shiga zanga-zangar nuna rashin jin dadi, kan shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliya da gwamnatin kasar sa ke fatan aiwatarwa.
Baya ga al’ummar kasar Japan, kasashen duniya da dama na bayyana rashin jin dadi, da kin yarda da matakin da gwamnatin Japan ke dauka, duk da haka, ‘yan siyasar gwamnatin kasar sun toshe kunnuwan su, sun kuma nemi hukumar IAEA da ta kimanta yanayin wannan ruwa, bisa samfurin da gwamnatin Japan ta gabatar mata bisa radin kanta.
To sai dai kuma hukumar IAEA hukuma ce dake tabbatar da amfani da makamashin nukiliya cikin lumana yadda ya kamata, wadda ba ta dace ba wajen aiwatar da aikin kimanta illolin da ruwan dagwalon nukiliya ka iya haifarwa ga muhallin teku da hallitu, kuma rahoton da ta gabatar bai kunshi cikakkun ra’ayoyin dukkanin masanan da suka shiga aikin kimanta shi ba.
Kamar dai yadda dan kasar Japan da muka ambata a baya ya fada, idan wannan ruwa ba zai gurbatta muhalli ba, to me zai hana gwamnatin Japan ta ajiye shi don yin amfani da shi? (Mai rubuta da zane: MINA)