Yayin taro na 53 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, an gudanar da muhawara ta gaggawa kan batun kona Al’qur’ani mai girma a wasu kasashe, inda aka zartar da kudurin da ya yi Allah wadai da lamarin da ya faru a bainar jama’a a baya-bayan nan.
Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na yau Alhamis cewa, kasar Sin na Allah wadai da kausasan kalamai game da sake kona Al’qur’ani mai girma da aka yi a wasu kasashe. A cewarsa, ya kamata a rika martaba ra’ayoyi da akidun mabambantan addinai.
Yana mai cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen duniya wajen aiwatar da shawarar wayewar kan bil Adama na duniya da neman daidaito da fahimtar juna da tattaunawa da dunkulewa tsakanin mabambantan al’ummu da kare bambancin dake akwai tsakaninsu, da kuma inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama. (Fa’iza Mustapha)