Sakamakon yawaitar samun mata masu juna biyu da suka je kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 da aka kammala, Hukumar Jindadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta yi barazanar sanya wa Hukumar Alhazai na wasu Jihohi takunkumi, da hukumomin da suka bai wa mahajjata masu ciki damar tafiya zuwa kasa mai tsarji domin aikin Hajji.
Kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da bayar da bayanai da ayyukan dakunan karatu na hukumar, Sheikh Suleiman Momoh ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai a Makkah.
- Yau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Emefiele Ya Shigar
- Jakadan Sin A Nijeriya Ya Gana Da Shugaban APC Ta Kasar
Akalla mata tara ne aka samu masu dauke da juna biyu a lokacin aikin Hajjin bana da aka kammala a tsakanin mata mahajjatan Nijeriya, daga ciki uku sun haihu daya kuma ta yi bari.
Sai dai Sheikh Momoh ya wanke hukumar NAHCON daga duk wani abu da ake zarginta da yi, yana mai cewa jami’an jiha ne ke da alhakin wannan abin kunya kuma za su fuskanci sakamakon abin da suka aikata.
“Idan muka koma Abuja, hukumar za ta binciki hanyoyin ladabtar da jihohin da suka bai wa alhazai masu ciki damar zuwa aikin Hajji.
“Za mu duba abin da ya cancanta ga wadannan jihohi kuma mu yanke shawarar matakan ladabtar da su. Muna da hanyoyi na cikin gida kan yadda za mu magance wadannan batutuwa.
Duk kuma irin hukucin da muka yanke, za mu sanar da ‘yan Nijeriya,” in ji Momoh.
Ya shaida wa manema labarai cewa NAHCON ta gudanar da gwaje-gwajen daukar ciki ga dukkan mahajjatan da suka zo ta hanyar gwajin ciki kuma an hana wasu mata biyu daga cikinsu zuwa aikin Hajji biyu wadanda aka tabbatar suna dauke da juna biyun.
Ya ce bisa binciken da aka yi, jami’an kiwon lafiya na hukumar jin dadin alhazai ta jihar sun ja hankalin jami’an jihohin, cewa wasu maniyyatan na da ciki amma sakataren zartarwa ya yi watsi da kiran ya kuma bai wa matan masu ciki damar zuwa aikin Hajjin.
Da yake jaddadawa a cikin bayanansa, ya ce za a gano irin wadannan jihohin tare da sanya musu takunkumi a kan haka, Suleiman ya nanata cewa NAHCON ba za ta bari jihohin su rika gudanar da nasu tsarin kiwon lafiya su kadai ba.
Shugaban tawagar likitocin NAHCON, Dakta Usman Galadima, ya bayyana cewa a cikin mata bakwai masu ciki da aka gano tun farko, daya ta haihu ne ta hanyar tiyata a lokacin da tayin danta ya kai wata bakwai, yanzu ta rasu) yayin da wata mata kuma cikin nata ya zube a sakamakon matsi irin na aikin Hajji.
Ya lissafa jihohin da aka samu mata mahajjatansu sun haihu wadanda mata ne guda bakwai, da suka hada da Sakkoto mutum (2), Katsina mace daya, Yobe mace daya, Adamawa mace daya, Kwara mace daya da kuma Filato mace daya.