Shugaban kungiyar nema wa nakasassu masu bukata ta musamman mafita da ke Kano, Abdulrazak Ado Zango ya ce dakagtar da albashin sabbin ma’aikata sama da dubu 10 da gwamnatin Injiniya Abba Kabir ta yi abun ya shafi nakasassu sama da 150 wanda ya sa suka shiga tsaka mai wuya.
Ya ce suna bukatar agajin gaggawa daga gwamnatin Kano ta biya su albashinsu, kasancewar su da ma ga halin da suke ciki na bukatar taimako tun da ba sa son bara kuma ba sa san barin makaranta, amma idan ba a taimaka musu ba a wannan hali, to fa an tauye kokarinsu na neman ilimi a manyan makarantu da jami’o’in kasar nan domin kuwa an dauke su aiki ne a bisa cancantarsu.
- Kiwon Lafiya: Yadda Dabi’un Ko-in-kula Ke Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke
- Kasar Sin: Ya Kamata A Martaba Mabambantan Addinai
Zango mai larurar rashin gani shugaban ne na makafi, guragu, kutare, kurmaye, Bebaye, Zabiya da masu, ya ce akwai bukatar aiwatar da dokar nan da aka zartar na cewa masu bukata ta musamman da za a kula da su kuma a rinka ware musu kasafin kudi duk shekara na kulawa da su da kuma dokar daukar su aiki kasha biyu cikin 100 a kowace ma’aikata a Jihar Kano.
Ya ce ya zama wajibi a aiwatar domin taimaka musu. Shugaban nakassun ya bayyana hakan ne a cikin wata hirar da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata a Kano.
A karshe, Zango ya yaba wa gwamnatin Abba Gida-gida kan kokarinta na bunkasa ilimi a Jihar Kano da kuma yunkurin fitar da wasu dalibai waje domin karo karatu. Ya ce akwai bukatar duk abun da za a yi wa al’umma na ci gaba a sa da masu nakasa. Ya ce akwai bukatar a nada nakassasu manyan mukamai a wannan gwamnatin.