Shugaban kungiyar manoman tumatur reshen Jihar Kano, Alhaji Dan Ladi Sani Yadakwari ya bayyana cewa, yanzu haka manoman tumatur sama da dubu 70 da ke Jihar Kano na bukatar tallafi daga sabon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida- gida) na tsaga dam-dam wato madatsun ruwa da ake da su a jihar wanda marigayi Alhaji Audu Bako ya yi su sama da shekara 50 da suka gabata.
A cewarsa, yin haka zai sa a samu guraran noman rani wadatattu a Jihar Kano da zai sa dubban matasan su samu aikin yi a wannan lokaci.
- Musabbabin Haramta Sana’ar Gwangwan A Jihar Borno
- Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Nadin Hafsoshin Tsaron Nijeriya
Yadakwari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin kungiyar manoman tumatur da ke Jihar Kano ranar Litinin da ta gabata.
Ya kara da cewa akwai bukatar gwamnan Kano ya nemi hadin kan Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki na tabbatar an hana shigo da tumatur daga kasashen ketarer.
Ya ce be shigowa da tumatir a Nijeriya ne dalilin da ya sa manoma ba sa nomansa yadda ta kamata har ya yi karanci, wanda hakan ce ta sa ya yi tsada da sauran kayan miya.
Haka kuma ya ce tsare-tsaren na tallafa wa manoma a gwamnatin baya tun daga matakin jiha da na tarayya abun a yaba ne kan kokarinsu na bunkasa noma a Kano da ma Nijeriya, musamman ma tsarin bunkasa noma na bai wa manoma rance ‘Anchor barrow’, wanda ya sa manoma da dama da suka san yadda ake abun suka samu duk da wasu masu shaci fadi a rediyo na cewa ba a bai wa wadanda suka dace ba.
“Shawararmu dai ga gwamnatocin kasar nan shi ne, a fito da tsarin ba da bashi ko tallafi a lokacin kaka wato lokacin girbi ta yadda za a bai wa mutum bashi gwargwadon abun da ya noma aka gani idan ma kara mai za a yi kashi 50 ko 100. Idan kuma ragi za a yi masa a kan abun da za a ba shi sai a yi hakan cikin tsari.”