Hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta ce kasar ta kara samun girbi mai armashi a bana, duk da illar tsanantar yanayi.
Alkaluman da hukumar ta fitar a yau Asabar, sun nuna cewa, jimilar hatsin da aka girbe a lokacin zafi na bana ya kai ton miliyan 146.13, wanda ya yi kasa da kaso 0.9 ko kuma ton miliyan 1.27 da ake samu duk shekara. Kana fadin gonakin da aka shuka hatsi a kasar Sin cikin shekaru 3 jere, ya karu zuwa kadada miliyan 26.61 a shekarar 2023.
Wani jami’in hukumar kididdigar Wang Guirong, ya bayyana cewa, domin karfafawa manoma gwiwar noman hatsi, gwamnatin kasar Sin na ci gaba da daga mafi karancin farashin alkama, haka kuma ta na samar musu da tallafi na lokaci guda.
Ya ce girbin mai armashi da aka samu zai shimfida tubalin daidaita yawan hatsin da ake samarwa a shekara, da samar da goyon baya mai karfi da zai inganta farfadowar tattalin arziki. (Fa’iza Mustapha)