Kasar Sin ta bukaci kasa da kasa da su kara bayar da muhimmanci ga gudunmuwar da samun ci gaba zai bayar wajen tabbatuwa da morar dukkan hakkokin bil Adama.
Shugaban tawagar Sin a MDD dake Geneva, Chen Xu ne ya bayyana haka a jiya Juma’a, yayin zama na 53 na majalisar kare hakkokin bil Adama ta MDD.
Chen Xu ya yi kira ga dukkan bangarori su shawo kan matsalolin dake tasowa ta hanyar amfani da sabbin dabaru yayin aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD, a matsayin wata hanya ta farfadowa daga mummunan tasirin annobar COVID-19.
A jawabinsa na gabatar da daftarin kuduri mai taken “ Gudunmuwar ci gaba wajen more hakkokin bil Adama”, Chen Xu ya nanata cewa samun ci gaba da kuma hakkokin bil Adama na dogaro da juna, tare da tabbatar da kasancewar kowannensu.
Kudurin, wanda ke kira ga dukkan kasashe su inganta ci gaba mai dorewa domin kyautata more hakkokin bil Adama, da cimma daidaiton jinsi da inganta damarmakin samun ci gaba ba tare da wariya ba, ya samu kuri’un amincewa 30, da 12 na rashin amincewa, da kuma wasu 5 da suka kaucewa kada ta. (Fa’iza Mustapha)