A yau Lahadi ne an wallafa sharhin da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin ya rubuta, game da zurfafa gyare-gyaren da ake yi a jam’iyyar da hukumomin gwamnati a kokarin da ake yi na zamanintar da tsari da karfin tafiyar da harkokin mulkin kasar Sin.
An wallafa sharhin a mujallar Qiushi ta bana karo na 14, mujallar kwamitin kolin JKS.
Sharhin ya bayyana cewa, zurfafa gyare-gyare a cikin jam’iyya da hukumomin gwamnati, wani muhimmin mataki ne na aiwatar da ka’idojin shirya babban taron wakilan JKS karo na 20, da matakan ciyar da zamanintar da tsarin kasar Sin da karfin tafiyar da harkokin mulki.
A cewar sharhin, sake fasalin zai sanya jam’iyya da hukumomin gwamnati dacewa da bukatun raya jam’iyyar da kasa baki daya. (Mai fassara: Ibrahim Yaya)