Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jagoranci raba kayan tallafi kayan abinci ga magidanta 13,000 wadanda matsalar harin Boko Haram ta shafa a garin Gwoza, da ke jihar.
Raba kayan tallafin abincin ya gudana ne a fargajiyar kofar Fadar Sarkin Gwoza, Mai Martaba Shehu Idrissa Timta.
- Zulum Ya Kaddamar Da Kwalejin Ilimi Ta Farko A Jihar BornoÂ
- Shehun Borno Ya Bukaci Jama’ar Jihar Borno Da Su Fito Rokon Ruwa
Gwamna Zulum ya shiga garin Gwoza ne ranar Asabar inda ya kai wata ziyarar ba-zata a babban asibitin garin da tsakiyar dare, wanda biyo bayan samun asibitin cikin duhu, ya bayar da umurnin daukar matakin gyara nan take.
Ranar Lahadi, Zulum ya jagoranci kaddamar da raba kayan tallafin ga mabukata, wanda kowane mutum daya daga cikin adadin magidanta 13,000 ya samu tallafin buhun shinkafa tare da na masara.
Gwamna Zulum ya samu rakiyar Darakta Janaral na Hukumar SEMA, Barkindo Mohammed Saidu, wanda ya jagoranci mika kyautukan zuwa ga wadanda suka ci gajiyar tallafin.