Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Girona sun cimma yarjejeniya kan siyan dan wasa Oriol Romeu.
Dan wasan zai rattaba hannu kan kwantiragi da kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.
- Man Fetur Da Ake Sha Ya Ragu Bayan Karin Farashi —NMDPRA
- Gwamnan Zamfara Ya Kai Wa Mangal Ziyarar Ta’aziyya
Wanda zai barshi a kungiyar har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2026.
Kuma an sanya batun siyansa kan Yuro miliyan 400 ga duk mai son siyanshi daga kungiyar kafin kwantiraginsa ya kare.
Dan wasan ya fara komawa Barcelona ne a shekara ta 2004, inda ya ci gaba daga makarantar horar da yan wasan Barcelona ta La Masia kuma ya samu shiga kungiyar farko ta Fc Barcelona kafin ya tafi Chelsea a shekarar 2011.
Romeu ya ci gaba da taka leda a Valencia, Stuttgart da Southampton
Daga nan ya koma Girona a shekara ta 2022 kuma ya taka rawar gani a kungiyar a kakar wasan data gabata.
Hakan ya sa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona ta yanke shawarar dawo da Romeu domin kara karfafa tsaron bayan kungiyar.