• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kiris Mahaifina Ya Sa A Kama Wanda Ya Fara Sa Ni Fim Amma… – Maryam Kimono

by Rabi'at Sidi Bala
2 years ago
in Nishadi
0
Kiris Mahaifina Ya Sa A Kama Wanda Ya Fara Sa Ni Fim Amma… – Maryam Kimono
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Daya daga cikin sabbin jaruman fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood Maryam Adam wadda aka fi sani da Maryam Kimono, ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta kafin shigarta cikin masana’antar Kannywood, ciki har da yadda mahaifinta ya kusa sa a kama wanda ya fara sa ta a fim kafin daga baya a warware matsalar. Kana jarumar ta yi kira ga masu kokarin shiga cikin masana’antar kan abubuwan da suka kamata su yi har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Ya sunan Jarumar?
Sunana Maryam Adam wadda aka fi sani da Maryam Kimono

Me ya sa ake kiranki da Maryam Kimono?
Saboda yawan saka kayan da nake yi

Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni ‘yar asalin Jihar Kano ce, an haife ni a unguwar Tukuntawa, na yi firamare da Sakandare a Tukuntawa, daga nan kuma sai na shigo harkar ‘industry’.

A wanne mataki kika tsaya a karatunki yanzu?
Na tsaya iya matakin sakandare ne

Labarai Masu Nasaba

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar kannywood?
Ni dai kawai fim yana burge ni ina son na ga ina ba da gudunmawa

Wacce irin rawa kike takawa cikin masana’antar?
Ina fitowa a fim, sannan yanzu na fara shirya wakoki, don akwai wakar da zan yi kwanan nan ni ce na shirya kuma zan yi ta nan ba da dadewa ba.

Idan na fahimce ki kina so ki ce har waka kike yi?
E, ina yin bidiyo din waka.

Ya za ki yi wa masu karatu bayanin yadda farkon wakarki ya kasance, da kuma irin kalubalen da kika fuskanta kafin fara wakar?
Ba waka nake yi ba bidiyo ne, idan mawaki ya yi waka na ji ta min dadi zan magana in ji yadda za a yi in saya, idan na saya sai in dauki nauyin shiryawa in biya duk wanda zan yi aiki da shi.

Maryam kimono

Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan kai kamar shekara biyu haka

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Da farko dai na samu matsala da babanmu saboda bai yarda in yi fim ba don har an kusa kama wanda ya sa ni a fim, amma daga baya da ya fuskanci kaddarata ce ta zo a haka, sai ya hakura ya ci gaba da yi min addua, to Alhamdu lillah yanzu dai komai na tafiya daidai.

Da wanne fim kika fara?
Na fara da fim din Gidan Dambe

Wace rawa kika taka cikin fim din?
Na taka rawar mataimakiyar jarumar da ta jagoranci fim din

Ya farkon farawarki ta kasance a lokacin?
Na je ‘Studio’ ne wani ya ganni ya ce zan dace da wata waka kawai muka fita aiki a gidanmu ma ba a sani ba ,shi ne farkon shiga ta matsala har babanmu ya sa a kama wanda ya sani.

To ya kika ji a lokacin da za ki fara kallon kyamara?
Ban ji komai ba saboda ina son yi, babban burina kawai shi ne in ga Kyamara a kaina, amma idan na tuna gida sai in ji babu dadi saboda na san dole sai na karbi hukunci.

Idan na fahimce ki kina so ki ce kin fara fitowa a bidiyon waka kafin ki fara fitowa a fim kenan?
Eh, kafin a barni a gida, a bidiyon waka na fara fitowa

Bayan da bidiyon wakar ya fita ya kika ji a lokacin, kasancewar a gida kin ce ba a san da hakan ba?
Bayan na yi waka da na tabbatar ga ranar da za a saki wakar hankalina ya tashi kuma na san zan karbi hukunci, kawai sai na gudu gidan yayar mamanmu ranar dai ban yi bacci ba saboda irin tashin hankalin da na shiga, can kuma gida ana ta tattauna ya za a yi a kamo ni.

Maryam kimono

To ya batun kalubale na ‘yan unguwa bayan da bidiyo ya bayyana, shin kin samu matsala daga gare su ko kuwa?
Kin san ai duk wanda ya ganka wage baki zai yi yana maka dariya ana ‘an ganki a waka, fim kika fara?’, to ni dai gaskiya ban fuskanci matsala da su ba tun da ba za su yi a gabana ba.

Daga lokacin da kika fara kawo iyanzu kin yi fina-finai sun kai kamar guda nawa?
A kalla dai na yi fim sun kai biyar.

Idan aka ce ki zabi bakandamiyarki cikin fina-finan da kika yi, wanne za ki dauka?
Na fi san ‘Gidan Dambe’, saboda a shi aka fara ganina har kuma na taka rawa.

Kafin ki fara fim, ko akwai abin da ya fara baki tsoro game da fim?
Gaskiya babu abin da ya bani tsoro, saboda babban burina in ga kyamara a kaina

Kamar irin maganganun da mutane ke yi akan ‘yan fim, shin bai tsorata ki ba?
Ko kadan, su ai mutane ko yaya ka yi sai sun yi magana, kawai ni ina son fim kuma ba ni da wani fargaba tun da har yanzu ban hadu da irin abubuwan da ake fada akan ‘yan fim ba.

Bayan shigarki cikin masana’antar ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta?
Gaskiya ban fuskanci wani kalubale ba saboda ina yin waka da kaina, kuma sannan wadanda suke kira na aiki ina da kyakkyawar alaka da su, tun da daga gida nake fitowa kuma idan na gama aiki gida nake komawa.

Wanne irin nasarori kika samu game da fim?
Alhamdullahi na samu nasarori sosai, saboda idan na je wuri ana iya gane ni, kuma sannan ina samun addu’oi marasa adadi a gun al’umma, babu abin da zan ce sai dai Alhamdullah.

Ya kika dauki fim a wajenki?
Na dauki fim a matsayin sana’a

Mene ne burinki na gaba game da fim?
Burina shi ne na daukaka.

Kina da ubangida a cikin masana’antar?
Eh, Director iliyasu Abdulmumini Tantiri.

Da wa kika fi so a hadaki a fim?
Duk wanda aka hada ni da shi zan iya aiki da shi kuma ina san kowa.

Wace ce babbar kawarki a Kannywood?
Ba ni da babbar kawa.

Kafin fara fim wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?
Hafsa idris yadda take aikinta yana burge ni.

Maryam kimono

Bayan da kika fara fim shin kun hadu da juna ko kun yi fim tare?
Ban yi fim tare da ita ba amma na neme ta kuma mun yi mutunci wanda har yanzu muna mutunci.

Yaushe kike sa ran yin aure?
A duk lokacin da aure ya zo min ina maraba da shi, saboda duk dan sunnan burinsa ya raya sunnah.

Ko akwai wanda ya kwanta miki a rai cikin masana’antar da har ta kai kun fara soyayya da shi?
Ina soyayya amma ban da saurayi a kannywood.

Misali wani ya fito ya ce yana sonki zai aure ki cikin masana’antar shin za ki amince, ko ba ki da ra’ayin hakan?
Shi aure ai nufin Allah ne ban san wanda zan aura ba, kuma ba ni da wani zabi kawai zabin Allah nake jira, don haka ko daga ina miji ya fito min ina maraba da shi.

Wanne irin namiji kike son aura?
Na fi son babban mutum, ina nufin mai shekaru.

Kamar shekara nawa kenan?
Kamar shekara Arba’in 40.

Wanne irin abinci da abun sha kika fi so?
Tuwo Miyar kubewa da Lemo Fanta.

Wanne irin kaya kika fi son sakawa?
Kimono.

Wacce shawara za ki ba wa masu kokarin shiga harkar fim?
Su shigo ta da kyakkyawar niyya kuma su sa a ransu sana’a suka zo yi, kuma su girmama na gaba da su, su zauna da kowa lafiya kuma su kiyaye mutuncinsu.

Wanne kira za ki yi ga sauran abokan aikinki?
Ban yi musu wani kira ba amma ina addu’a Allah ya hada kanmu baki daya.

Wacce irin matsala kuka fi fuskanta cikin masana’antar?
Rashin hadin kai.

Maryam kimono

Ko kina da wani kira da za ki yi ga gwamnati game da ci gaban masana’antar?
Ina kira ga gwamnati da ta tallafa wa masana’antar da kayan aiki kuma ta bude makarantar koyon harkar ta dauki malamai.

Me za ki ce da masoyanki?
Ina yi musu fatan alkhairi da wanda na sani da wanda ban sani ba.

Me za ki ce da makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Su ma ina yi musu fatan alkhairi.

Me za ki ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Allah ya kara muku daukaka.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaida babarmu da babanmu da ‘yan uwa da abokan arziki.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sir Sherard Cowper-Coles: Biritaniya Da Sin Suna Amfana Daga Karuwar Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Tsohon Ministan Yada Labarai, Maku A Nasarawa

Related

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro
Nishadi

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

6 hours ago
Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage
Nishadi

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

9 hours ago
Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe
Nishadi

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe

1 week ago
Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
Nishadi

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje

2 weeks ago
Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda
Nishadi

Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda

2 weeks ago
Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri
Manyan Labarai

Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri

2 weeks ago
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Tsohon Ministan Yada Labarai, Maku A Nasarawa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Tsohon Ministan Yada Labarai, Maku A Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

May 11, 2025
Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

May 11, 2025
Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

May 11, 2025
Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

May 11, 2025
2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC

INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta

May 11, 2025
Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

May 11, 2025
Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

May 11, 2025
Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci

Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci

May 11, 2025
Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali

Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali

May 11, 2025
Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU

Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU

May 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.