Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta fafata da Afirka ta Kudu da Benin da Rwanda da Zimbabwe da kuma Lesotho a wasannin rukuni na uku na gasar cin kofin duniya da za’a yi a shekara ta 2026.
A ranar Alhamis ne aka gudanar da bikin fitar da jadawalin wasannin a birnin Abidjan na kasar Ibory Coast wadda ita ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara mai zuwa.
- Sau 14 dai kasashen Nijeriya da Afirka ta Kudu suka fafata tsakanin su, inda Super Eagles ta yi nasara sau bakwai sannan suka yi canjaras biyu kuma karo na karshe da Nijeriya ta kara da Afirka Ta Kudun a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya shi ne kafin gasar 2010.
Super Eagles ta samu nasara a wasanni biyu da suka fafata, amma Afirka ta Kudu ta samu gurbin shiga gasar la’akari da matsayin mai masaukin baki kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya ta tsara.
Kasar Senegal, zakarun Afirka, na rukunin na biyu ne tare da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo da Togo da Mauritania da Sudan da kuma Sudan ta Kudu.
Sai Kasar Morroco, wadda ta kai wasan dab da karshe a gasar kofin duniya da aka buga a Katar – ta samu kanta a rukuni na biyar inda za ta kara da Zambia da Tanzania da Congo Brazzabille da Jamhuriyar Nijar da kuma Eritrea.
Ghana tana rukuni na daya tare da Mali, da Madagascar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Comoros da kuma Chadi kuma nan gaba kadan za’a saka ranar fara wasannin.
Cikakken Rukunin:
Rukuni na A: Masar, Burkina Faso, Guinea-Bissau, Saliyo, Ethiopia, da kuma Djibouti.
Rukuni na B: Senegal, Democratic Republic of Congo, Togo, Mauritania, Sudan da kuma Southern Sudan.
Rukuni na C: Nijeriya, Afirka ta Kudu, Benin Republic, Zimbabwe, Rwanda da kuma Lesotho.
Rukuni na D: Kamaru, Cape Berde, Angola, Libya, Eswatini da kuma Mauritius
Rukuni na E: Morroco, Zambia, Tanzania, Congo Brazzabille, Nijar da Eritrea.
Rukuni na F: Ibory Coast, Gabon, Kenya, Gambia, Burundi, da kuma Seychelles
Rukuni na G: Algeria, Guinea, Uganda, Mozambikue, Botswana, Somalia
Rukuni na H: Tunisia, Ekuatorial Guinea, Namibia, Malawi, Liberia, Sao Tome e Principe.
Rukuni na I: Ghana, Mali, Madagascar, the Central African Republic, Comoros da Chad. Za’a fara buga wasannin daga ranar 3 ga watan Nuwamban wannan shekarar
ta 2023, zuwa ranar 18 ga watan Nuwamban 2025 kuma kasashen Afirka na da gurbi tara, bayan da aka kara adadin kasashen da za su shiga gasar da za’a buga a shekarar 2026 zuwa 48.
Za dai a buga gasar a kasashen Amurka da Medico da kuma Canada daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026, kasar Argentina ce dai ke rike da kofin gasar da ta dauka a shekarar 2022 da aka buga a Katar.