Allah Ya yi wa tsohuwar kwamishiniyar kasafin kudi da tsare-tsare, sannan kuma Kwamishiniyar harkokin mata, a lokacin mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na farko, Barista Zubaida Damakka Abubakar.
A wata hira da wani makusancin tsohon Kwamishiniyar, Abubakar Aminu Ibrahim ya shaida wa NIGERIAN TRACKER cewa Barista Zubaida ta rasu ne a yau a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.
- Gini Ya Yi Ajalin Yara 2 Legas
- Ziyarar LEADERSHIP Hausa A Hubbaren Degel Ta Mahaifin Shehu Usman Danfodiyo
Tsohuwar Kwamishiniyar ta haura shekaru 45 kuma ta rasu ta bar ‘ya’ya uku da miji.
An yi jana’izarta a Kano a ranar Lahadi da misalin karfe 9 na safe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp