Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya amince da wani shirin bayar da tallafi na biliyoyin nairori ga ma’aikatan jihar domin rage radadin cire tallafin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.
Tallafin wanda babban sakataren yada labarai na gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya kaddamar a wani taron manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar a ranar Litinin, an raba shi sassa daban-daban da ke karkashin gwamnati a fadin jihar.
Tare da tallafin, akwai tallafin kudi na Naira 10,000 ga kowane ma’aikacin gwamnati a jihar, wanda za a fara kaddamar da shirin a wannan watan kuma zai ci gaba har sai an bullo da shirin sabon mafi karancin albashi.
Ajakaye ya ce an dauki matakin ne domin rage wa ma’aikata kalubalen da suke fuskanta kan tabarbarewar tattalin arziki da cire tallafin man fetur ya haifar a fadin Nijeriya.