Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta sanar da cewa, ta fara aikin tabbatar da ingancin ruwan sha a yankunan karkara, tana mai bukatar sassa masu ruwa da tsaki su aiwatar da bincike domin gano matsalolin dake da alaka da ruwan sha a karkara, da karfafawa da inganta matakin wadatar ruwan sha a yankunan.
A baya-bayan nan ne ma’aikatar ta gudanar da taro a gundumar Yingshan na lardin Hubei domin inganta amincin ruwan sha. Taron ya shawarci sassa masu ruwa da tsaki su aiwatar da cikakken bincike da karfafa hanyoyin gano matsaloli da aiwatarwa da inganta bincike akai-akai da sa ido kan batutuwan da suka shafi amincin ruwan da inganta warware matsalolin da aka gano. Haka kuma, an bada shawarar mayar da hankali kan bangarorin dake bukatar gyarawa na samar da ruwa, da aiwatar da dabaru bisa matakan raya dunkulewar birane da karkara, da aiwatarwa da inganta dabaru masu dorewa na tabbatar da ingancin ruwan sha a yankunan karkara.
Rahotanni na cewa, ma’aikatar ta gudanar da taruka biyu a baya-bayan nan, domin nazari da warware matsoli daya bayan daya, da samar da dabaru masu dorewa da kuma aiwatar da ayyukan da za su shawo kan karanci da matsalolin samar da ruwan sha a yankunan karkara. (Fa’iza Mustapha)