Wasu rahotanni na cewa, a baya bayan nan daraktan hukumar leken asiri ta Amurka (CIA), William Joseph Burns, ya bayyana cewa Amurka ta samu ci gaba, wajen sake gina tsarin leken asiri a kasar Sin, kuma tana aiki tukuru wajen inganta kwarewar ma’aikata na tattara bayanan sirri.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a taron manema labaru da aka saba yi a yau Litinin cewa, kasar Sin ta lura da rahoton, kuma ta damu da lamarin. Jami’ar ta ce Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye tsaron kasa.
Mao Ning ta yi nuni da cewa, Amurka ta sha yada bayanan karya game da abin da take kira da ‘yan leken asiri na kasar Sin da hare-haren intanet, a sa’i daya kuma, ta fito fili tana ikirarin aiwatar da manyan ayyukan leken asiri kan kasar Sin, wanda hakan ya nuna cikakken halin ta.
(Mai fassara: Bilkisu Xin)