Joy Bishara, daya daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace, wadda maharan Boko Haram suka sace ta da wasu a garin Chibok a Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu 2014, an ranar aurenta a kasar Amurka.
Idan za a iya tunawa jimillar dalibai mata 276 ‘yan kungiyar ta’addan suka yi garkuwa da su.
- ‘Yan Adawa Ku Zo Mu Yi Aiki Tare A Katsina – Mai Ba Gwamna Shawara
- DSS Na Shirin Sake Kama Emefiele Bayan Bayar Da Belinsa —Lauyoyi
Kimanin ‘yan matan makarantar 57 ne suka tsere daga hannunsu.
Sojojin Nijeriya sun ceto wasu amma sama da ‘yan mata 100 ne har yanzu suka bace.
Sai dai kuma, Bishara da ‘yar uwarta, Lydia Pogu, wadanda suka tsere daga hannun Boko Haram, sun koma Amurka da zama.
Ta yi karatu a Jami’a, inda ta samu digiri a fannin zamantakewa a 2021.