Wutar Dajin Girka ta ci gaba da tsananta a rana ta biyar bayan tashinta, lamarin da ya tilasta kwashe mutane fiye da dubu 30 daga tsibirin Rhodes, a dai dai lokacin da masana ke ci gaba da gargadi kan illar dumamar yanayi a bangare guda tsananin zafi ke ci gaba da ta’azzara a kasashen Turai.Â
Girka, Birtaniya Spain da kuma Amurka na sahun yankunan da suka fi fama da matsalar ta wutar daji wadda masana ke alakantawa da dumamar yanayi wadda a shekarun baya-bayan nan ta ke ci gaba da tsananta tare da barazana ga tsirrai da halittun ban kasa.
- Nijeriya Na Bukatar Gudunmawar Sarakunan Gargajiya Don Farfado Da Darajarta – Hon. Abbas
- Sabida Siyasa Aka Dakatar Da Ni – Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa
Wani rahoton kwararru tun gabanin tsanantar wutar dajin ta Girka da ta shiga kwana na shida a ranar Talata ba tare da kakkautawa ba, ya yi gargadin fuskantar tsananin zafi a kasashe daban-daban ciki har da Turai Australia da Arctic baya arewaci da kudancin Amurka.
A cewar kwararrun, tsananin zafin da duniya ke gani ya jefa yiwuwar ceto dazuka daga gobara a hatsari fiye da kowane lokaci a tarihi.
Baya ga gobarar dajin ta Girka a tsibirin Rhodes da Corfu can a Kanada dazuka da dama ke fama da wutar da zuwa yanzu ta kone fiye da muhalli dubu 25 kwatankwacin wadda kasashen Chile da Australia suka gani a farkon shekarar nan.