Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta bankado ma’aikatan da aka dauka aiki da takardun bogi guda 1,618.
Shugaban ma’aikatan tarayya Folashade Yemi-Esan, ta bayyana hakan a taron manema labarai kafin gudanar da makon ma’aikata na 2023.
- Jami’an Tsaro Sun Tsare Shugaban Nijar Kan Fargabar Yunkurin Juyin Mulki
- NLC Ta Bai Wa Tinubu Kwanaki 7 Don Dawo Da Tallafin Mai, Ko Ta Shiga Yajin AikiÂ
Folashade wadda ta sanar da hakan a jiya Talata ta ce, gwamnatin ta bankado ma’aikatan ne a cikin tsarin biyan albashi na IPPIS.
Kazalika, shugabar ta ce, an kuma gano wasu ma’aikatan su 69,854 a wasu manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma hukumomin gwamnatin tarayya da ke shiyyoyi shida na kasar nan, ciki har da babban birinin tarayyar Abuja.
Ta kara da cewa, bisa aikin da ake ci gaba da gudanarwa, an dakatar da wasu ma’aikatan daga cikin tsarin IPPIS.
Kazalika Folashade ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya na kan aiki sabunta alawus-alawus na tafiye-tafiyen ma’aikata.
Ta sanar da cewa, “Kwamitin fadar shugaban kasa na daidata albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.”
Kazalika ta ce, majalisar zartarwa ta amince da kashi 40 a cikin dari na gundarin albashin ma’aikatan wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba.