Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karrama Hajiyar da ta mayar da kudin da ta tsinta dala 80,000 a aikin hajjin da ya gabata a Saudiyya.
Hajiya Aishatu ‘yan Guru Nahuce daga karamar hukumar Bungudu ta samu dala 80,000 wanda yayi daidai da kudin Nigeriya (N64,240,000) sannan ta mika su ga jami’in hukumar jin dadin alhazai ta Zamfara domin maida wa mai shi.
- Da Dumi-dumi: Tinubu Ya Mika Wa Majalisa Sunayen Ministoci 28
- Juyin Mulki: Amurka Ta Bukaci Gaggauta Sakin Bazoum
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyyana haka a takardar da ya sanya wa hannu ga manema labarai yau a Gusau.
A cewarsa, Gwamnan ya kuma bayyana matukar farin cikinsa da gwamnatin jihar ta nuna a kan kyakyawan halin Hajiya Aisha da ta maida kudin.
“Dukkan al’ummar jihar Zamfara suna alfahari da farin ciki kan abin da Hajiya A’ishatu ta yi a Saudiyya, ta karawa jiharmu da kasa baki daya kima da daraja a idon duniya.
“Mun ga kyakyawan misali karara na gaskiya da ya kamata a yi koyi da Hajiya Aisha, don ba kowa ne zai iya samun irin wadannan makudan kudade a wurin da ba kowa, ya mayar da su.
“Don haka gwamnatin jihar Zamfara za ta yi iyaka kokarinta don taimaka wa iyalan Hajiya Aisha.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma zai karrama Hajiya Aisha bisa wannan aiki na gaskiya.”
Tun da farko, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin gabatar da Hajiya Aisha, ya jaddada cewa, matakin da ta dauka ya kara kara mutunta al’ummar Zamfara baki daya.
Hajiya Aisha ta nuna godiyarta a kan karamci da aka yi mata tun daga Saudiyya zuwa yanzu.