Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a ranar Alhamis ya yi kira da a gaggauta sakin shugaban Nijar, Mohamed Bazoum.
“An tsige Bazoum daga kan karagar mulki”, a cewar wasu gungun sojoji da suka bayyana a gidan talabijin na kasashen Afirka ta Yamma da yammacin jiya Laraba, sa’o’i kadan bayan sun tsare shugaban a fadar shugaban kasa.
Blinken ya bada wannan umurni ne a wani taron manema labarai a Wellington babban birnin kasar New Zealand cewa “ba zai iya tantance wa ba ko wannan juyin mulkin halastacce ne ko bai halasta ba, hurumin lauyoyi ne su tantance.
“Amma dai, abin da ya bayyana a fili shi ne, yunkurin kwace mulki da karfi da kuma kawo cikas ga kundin tsarin mulkin dimokuradiyya”
Don haka, Blinken ya yi kira da a gaggauta sakin shugaba Bazoum.