Ya zuwa ranar Laraba 29 ga watan Yuni 2022, Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON ta samu nasara jigilar Maniyyata fiye da dubu 20,669 daga cikin kujeru 43,008 da aka ware wa jihohin Nijeriya, wannan kuma babbar nasara ce musamman ganin yadda wa’adin kammala jigilar maniyyata daga sassan duniya zuwa kasa mai tsarki ke kara matsowa, wannan ya sa hukumar alhazai karkashin jagorancin Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ke kara kaimun ganin ta kammala kafin a rufe filin jiragen sama na kasar Saudiya.
An samu kwashe Maiyyatar ne a sawu fiye 38 da jiragen sama suka yi daga jihohi 19 da birnin Abuja da kuma tawagar rundunar sojojin Nijeriya ta kamfanonin jiragen sama guda uku da suka hada da Mad Air; Azman Air da Fly Nas, wadanda sune aka dora wa alhakin wannan aiki a wannan shekarar.
Jihar Sakkwato ne a kan gaba na yawan wadanda suka isa kasar mai tsarki da alhazai 1,630, Adamawa nada 1,117; Bauchi 1,303, Benuwai 101; Borno 1,040; Ekiti 136; Abuja 1,535; Gombe 547; Kaduna 793, Katsina 554. Saura sun hada da Kebbi 412; Kogi 361; Kwara 1,100; Lagos 1,598; Ogun 467; Ondo 249; Osun 577; Oyo 340; Yobe 795, Zamfara 1,191, Kano, 339 yayin da zuwa yanzu an yi jigilar jami’an tsaro 329 suwa kasa mai tsarki.
Daga cikin Maniyyatar da suka isa kasa mai tsarki ‘yan Nijeriya 12,860 sun dira garin Madinah don gudanar da ibadoji da ziyara yayin da kuma 4,119 suka isa garin Jeddah tun da aka fara jigilar farko a ranar 9 ga watan Yuni daga filin jiragen sama na kasa da kasa da ke Maiduguri babbar birinin Jihar Borno.
Haka kuma bincike ya nuna cewa, bayan Alhazai 11,801 da suka kai ziyara garin Madinah, 5,178 daga cikin su sun riga sun wuce garin Makkah a cigaba da shirye-shiryen ayyukan hajjin bana a kasa mai tsarki.
Ganin yadda wa’adin da kasar Saudiya ta gindaya na kwashe maniyyata nata karatowa kuma gashi akwai maniyyata da dama da basu san halin da suke ciki ba, ga kuma wadanda suka biya kudaden su ta kamfanonin jirgin yawo, wanna ya sa hukumar Alhazai NAHCON ta yanke shawarar garzayawa wajen hukumar kasar Saudiya don neman karin kujeru ta yadda dukkan wadanda suka biya kudadensu ta kowacce hanya za su samu sauke farali, hakan ya sa ta tura wata kakkarfar tawaga kasar Saudi Arabiya don nema wa Nijeriya karin kujeru a aikin hajin bana.
Tuni Kwamishina aikin hajji mai kula ayyuka, Abdullahi Hardawa, ya gana da mataimakin Minista mai kula da aikin Hajji da Umara a kan lamarin ranar Lahadi.
A tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, Hardawa ya ce, an mika wa hukumar kasar Saudiyan bukatar kujera 5,000, saboda kanin al’umma sun samu sauke farali a bana.
“Ina Saudiya a halin yanzu ne don neman karin kujeru wanda muka tura bukatar haka tun kafin a fara harkokin aikin hajjin bana.
“Daga sauka ta Riyadh na wuce don ganawa da Ambasadan mu wanda ya bayyana mani irin kokarin da ya ke yi a kan lamarin.
“Sun tabbatar mani da cewa, za su amince da bukatarmu tunda mun riga mun rubuta musu, sun yi alkawarin biya mana bukata.
“Muna bukatar wadannan kujerun ne domin kamfanoni masu jigilar alhazai da kuma maniyyata a jihohi da kuma na bangaren gwamnatin tarayya.
“Bamu taba tunanin za a nemi karin kujerun hajji ba saboda yadda aka kara kudin zuwa hajjin a bana,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, ya kawo ziyarar zuwa kasa mai tsarki don a kara karfafa bukatar samun kujerun aikin hajjin don al’umma da dama su samu zuwa sauke faralin.
Sai dai a ranar Talata 28 ga watan Yuni 2022 NAHCON ta sanar da cewa, bata samu nasarar neman karin kujerar da suka yi ba, kuma daga yanzu hukumar Saudiyya ta haramtawa duk wanda ya kai shekara 65 kasancewa a cikin masu taimaka wa Alhazai.
Ta bayyana cewa, duk kokarin da hukumar ta yi na samun karin kujerun ya ci tura. Kujeru 43,000 ne aka ba Nijeriya inda aka raba a tsakanin jihohi 36 da Abuja da kuma rundunar sojojin Nijeriya da wasu kamfanonin jigilar alhazai masu zaman kansu.
Amma saboda rikicin da aka samu a tsakanin NAHCON da wasu kamfanonin jigilar na yadda suka yi korafin kujerin da aka basu bai ishesu ba ya sa NAHCON ta garzaya Saudiya don neman karin kujerun don a warware matsalar amma sai gashi hukumar Saudiyya ta ki amincewa da wanna bukatar.
Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara ta bayyana haka a sanawar da ta sanya wa hannu a ranar Talata a Abuja.
•Wasu Ka’doji Sun Canza A Bana
Shugaban Kanfanin zirga-zirgar Alhazai ta ‘Comerel Trabels and Tours Limited’, Ustaz Abubakr Siddeek Muhammad, ya nemi ‘yan Nijeriya masu tafiya sauke farali a bana dasu yi hattara don akwai wasu sabbin dokoki da ka’idoji da kasar Saudiya da aka gindaya wajen ayyukan Haji a bana musamman ganin tasirin annobar cutar Korona da aka fuskanta a shekarar bara.
Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a taron fadakar da Maniyyata da aka yi a Abuja a makon daya wuce, a wanna shekara gwamnatin kasar Saudiyya ta sanya ido a kan dukkan harkokin da suka shafi ayyukan hajji, ta yadda in banda abin da ya shafi ayyuka na ibada duk an canza dokokin da ke tattare da su. Ya ce, an yi wannan ne do a kara ingata harkokin ayyykan hajji da kara jin dadin Alhazai.
Idab za a iya tunawa an dakatar da baki masu zuwa aikin haji daga kasashe duniya a shekarar 2019, 2020 da kuma 2021 saboda annobar cutar Korona da duniya ta fuskanta.
Wannan ne ya sa hukumar kasa Saudi Arabia ta kayyade masu zuwa hajji a shekarar zuwa mutum 1,000 ‘yan asalin kasar da kuma mutum 10,000 daga wasu kasashe da suka zaba a shekarar 2021.
“An canza abubuwa da dama a cikin shekara uku da suka wuce, sun kuma hada da ayyukan Muassassah wadanda a da suka aiki tare da hukumomin alhazai na jihohi, inda suke samar da musu ayyukan kula da jin dadin alhazai da sauransu.
“A halin yanzu ana gudanar da ayyukan ne daga kwamiti na tsakiya inda daga nan ne za a rinka bayar da odar yadda za a gabatar da aikin wannan kuma wani sabon abune ga masu tafiyar da aikin haji da ma alhazan gaba daya. Saboda haka yakamata kowa ya fahimci wannan dokokin a kamu karbe su a mastayin ayyukan ibada,” inji Ustaz Abubakr.
Ya kuma ce a da ana samun tanti mai lamba ‘tent A’ dadai sauransu amma a wannan shekarar an samar da ‘tent A’ da ‘tent D’ kawai don amfanin Alhazai.
Ya kuma yaba wa Shugaban Hukumar Alhazai (NAHCON) Alhaji Zikrullah Kunle Hassana kokarinsa na tabbatar da an samu nasarar aikin Hajj a wannan shekarar, ya kuma nemi hukumar ta tabbatar da jajircewarta wajen jin dadin alhazai kamar yadda ta saba.