Rundunar ‘yansanda a Jihar Nasarawa ta yi nasarar café wasu mutu biyu a bisa zarginsu da laifin satar wata mota a Karamar Hukumar Lafia dake jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar DSP Rahman Nansel, shi ya bayyana hakan ga manema labarai a Lafia babban birnin jihar.
Nansel ya bayyana cewa barayin su biyu da mai shekara 49 da kuma mai shekara 38 , bayan sun saci motar sai suka gudu zuwa zuwa Taraba da Filato, amma saboda kwazon jami’anmu suka matsa kaimi sai da suka kamo su.
Ya ce, “A ranar 19 ga Yuli da misalin karfe 4 na yamma, wani ya shigar da korafin sace masa mota a ofishin ‘yansanda na ‘B’ Dibision da ke Lafia, cewa an sace masa mota kirar Toyota Corolla, 2015 da aka ba wa bakanike gyara.
“Duk da haka, wadanda ake zargin su gudu da motar zuwa wani wuri da ba a sani ba, kuma an yi kokarin ganin an isa wurin amma hakan ya ci tura.
Duk da haka runudunar ‘yansandan ‘B’ Dibision ba su yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da bincike ba.
“Saboda haka, daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Sani Labaran mai shekaru 49 an bibiye shi kuma a kan hanyar Shinge, Lafia, kuma an kama shi a Gembu, jihar Taraba, yayin da aka kama abokin aikinsa Ibeto Nwobodo mai shekaru 38 a Faringada, Jos a garin Jos.
“A yayain gudanar da bincike wadanda ake zargin sun amsa laifinsu inda suka ce sun sayar da motar akan kudi Naira miliyan 2.5.”
Nansel ya kara da cewa kwamishinan ‘yansanda, Maiyaki Baba, ya yaba wa jami’an ‘yansanda da suka gudanar da wannan aiki, ya kuma ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.