A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi maraba da baki dake halartar wasannin jami’o’in duniya na bazara karo na 31 ta FISU a birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.
Xi ya yi fatan cewa, matasa daga sassa daban-daban na duniya za su yi amfani da damar gasar ta wasannin jami’o’in duniya dake gudana a Chengdu wajen kara fahimtar juna da kuma kara sanya sabbin kuzari ga ci gaban bil’adama.
Ya ce, kasar Sin ta cika alkawuran da ta dauka na tabbatar da tafiyar da harkokin wasannin na Chengdu lami lafiya, ta hanyar gudummawa da ta bayar wajen raya harkokin wasanni na matasa na kasa da kasa.
Kasar Sin ta yi maraba da dukkan baki da suke halartar wasannin jami’o’in duniya na bazara ta FISU karo na 31, don fahimta da cin moriyar zamanatarwa ta kasar Sin. (Yahaya Babs)