Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bukaci sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar da su koma barikinsu tare da mayar da mulkin farar hula a kasar cikin kwanaki 15.
Cikin wata sanarwa da kwamitin tsaro da zaman lafiya na AU ya fitar, ya yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojojin suka yi a Nijar.
- Zulum Ya Cire Sunan Ngoshe Daga Sunayen Kwamishinonin Borno
- Burin Sheikh Dahiru Bauchi Daya Tak Da Ya Rage Masa -Sayyadi Aliyu
Sanarwar, ta yi dai-dai da ta tarayyar Turai wadda ta dakatar da aikin tallafi a kasar.
Sashen Hausa na BBC, ya ruwaito cewa hakan na zuwa ne yayin da ECOWAS ke shirin gudanar da taro ranar Litinin mai zuwa kan juyin mulkin da aka yi a Nijar.
Kasashen duniya da dama na ci gaba da yin Allah-wadai kan juyin mulki da dakarun sojin kasar suka yi.
Nijar dai ta shiga jerin kasashen yankin Sahel da sojoji suka karbe ikon gudanar da mulki.
A nasa bangare sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce Amurka za ta dakatar da tallafin miliyoyin daloli da ta ke bai wa Nijar.
Nijar wadda ke yankin Sahel ta kasance babbar kawa ga kasashen yamma a kokarin da suke yi na yaki da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel da ke yammacin Afirka.
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu na shirin karbar bakuncin taron kungiyar shugabannin kasashen yammacin Afirka domin tattauna batun juyin mulkin na Nijar.
A ranar Laraba da daddare ne sojojin Nijar suka ayyana kifar da gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum, bayan da suka tsare shi da shi a fadar shugaban kasa.
Daga baya shugaban dakarun fadar shugaban kasar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban mulkin sojin kasar.