Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji sun yi luguden wuta ta sama a sansanonin kasurguman ‘yan bindiga Ado Aliero da Dankarami da ke jihohin Katsina da Zamfara, inda suka samu nasarar kashe ‘yan bindiga sama da 16.
A cewar wata majiyar rundunar sojin ta sama, sojojin sun yi wannan luguden wutar ne a tsakanin ranar 28 zuwa ranar 29 ga watan Yulin 2023 a sansanoni daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Tsafe da ke a jihar Zamfara da kuma Faskari da Jibiya da ke jihar Katsina.
A luguden wutan da sojin suka yi a Zurmi, sojojin sun kashe akalla ‘yan bindiga 16 wadanda aka tabbatar cewa, yaran kasurgumin dan bindiga ne mai suna Dankarami.
Kazalika, majiyar ta ce, sojojin sun kuma yi wani luguden wuta a sansanin kasurgumin dan bindiga Ado Aliero da ke kusa da tsaunin Asola da ke karamar hukumar tsafe a jihar Zamfara.
Sojin sun yi luguden wutar ne, bayan samun bayanan sirri cewa, Ado da yaransa sune a kwanan baya suka sace mutane da wasu Shanu a Tsafe da Faskari.
Wani manomi mai suna Mallam Kabiru Umaru da ke daura da Tsafe, wanda kuma ganau ne lokacin da sojin ke luguden wutar ya ce, sojojin sun lalata sansanin ‘yan bindigar, inda ‘yan kadan daga cikinsu suka iya arcewa daga sansanan.
Kakakin rundunar ta sojin sama Komodo Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai harin a sansanan na ‘yan bindigar biyu.