Yau dai muna tafe da labarin wata kabila da a shekarun baya suke bauta wa Talotalo. Yanzu a wannan zamanin ana kiwata Talotalo ne kayan ci ko abinci, ba kamar zamanin 300 BC ba, wanda a lokacin a ke kallon tsuntsayen Talotalo a matsayin wasu alloli kuma ababen girmamawa.
Hasali ma su Talotalo tsuntsayen gida ne da ake amfani da su wajen ciyar da mutane yayin ranekun ibada na addini, amma su a wancan lokacin su a ke dauka ababen bauta. ‘Yan Addinin Maya da al’adunsu sun kasance suna daukar Talotalo a matsayin muhimman abubuwa kuma ababen bauta.
A yanzu dai Talotalo ko in aka je za ka same su cikin kayan tarihi na Maya da kuma zane-zane. Tsohuwar al’ada Maya na daya daga cikin ci gaban wayewa a zamanin nan, inda kuma babban sashe na al’adunsu shi ne kaunar Talotalo.
Ana kimanta matsayin Talotalo da Alloli bauta. Haka kuma wani mulkin Maya ya hada da kalmar “turker” a cikin sunan lakabi na sarautarsu a lokacin.
“Wadannan tsuntsaye a zamanin farko masu hannu da shuni ne kawai suke iya mallaka,” in ji Kitty Emery, Mataimakiyar Mai Kula Da Ilimin Kimiyya da Muhalli a Gidan Tarihi na Florida. A 2012, Emery ta kasance wani bangare na kungiyar masu bincike wadanda suka buga.
Wata takarda da ta bayyana shsidar shigar da Talotalo ta farko cikin jerin tsuntsayen da za’a ci. Yayin binciken, tawagar ta gano wani Talotalo daban a El Mirador, a tsohuwa ‘yar Kabilar Maya da suka kasance a gida da mutane kusan 200,000.
Mazauna El Mirador, da ake kira Guatemala, suna suna rayuwa a cikin magudanar ruwa ta hanyoyi masu ban mamaki. Amma sun yi wani abu daban na ban mamaki, shi ne bautar Talotalo, ko da yake Maya suna shigo da Talotalo ne daga Medico. Har ila yau, suna daraja Talotalon da yake yawo a yankin El Mirdor. Ana kimanta gami da daraja wadancan tsuntsunaye ne daidai da kyawun fuka-fukansu da kawuna msu launuka iri-iri, amma ba sa taba kiwata shi a cikin gida.
Yadda ake kallon Talotalo yana da muhimmanci ga Maya, Emery ya ce, suna karfin iko.