Chelsea ta sayi matashin dan wasan tsakiyar Faransa, Lesley Ugochukwu daga Rennes kan kwantiragin shekaru bakwai a kan kudi Yuro miliyan 27 (£23.2m).
Ugochukwu, mai shekaru 19, ya buga wa Rennes wasanni 47 a gasar Ligue 1, kuma ya buga gasar Europa.
- Bana Iya Barci Saboda Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki -Tinubu
- Jirgin Kashe Gobara Kirar Sin Ya Kammala Gwajin Tashi Na Farko
Har yanzu bai fara bugawa Faransa wasa ba amma ya buga wa Les Bleus wasa a matakin yan kasa da shekara 17 da kasa da 18 da kuma yan kasa da shekara 19.
Zuwan nasa ya zo ne bayan kocin Chelsea Mauricio Pochettino kwanan nan ya ce Blues na bukatar kara karfafa ‘yan wasan tsakiyarsu.
Ugochukwu, wanda ya fara taka leda a babbar tawagar Rennes bayan cika shekaru 17 da haihuwa yayi matukar kokari a wasannin da ya bugawa Rennes.
Chelsea na da wani shiri na sayen matasa masu hazaka da za su iya zama taurarin kwallon kafa na duniya a nan gaba.
Yarjejeniyar Ugochukwu kuma tana da zabi na karin wata shekara idan ya tabuka.
Daraktan wasanni na Chelsea Laurence Stewart da Paul Winstanley sun ce: “Shi [Ugochukwu] matashi ne mai ban sha’awa wanda ya riga ya taka rawar gani a gasar Ligue 1.
“Mun ji dadin kasancewar Lesley tare da mu kuma zai samu damar hadewa da tawagar cikin sauri.”
Rahotanni sun ce Blues na neman dan wasan tsakiyar Brighton Moises Caicedo.