A baya-bayan nan, gwamnatin Japan ta fitar da takardar bayani ta shekarar 2023 dangane da tsaro, inda ta yi ikirarin “fuskantar yanayin tsaro mafi tsanani da sarkakkiya tun bayan yakin duniya na biyu”, tare da bayyana kasar Sin a matsayin “babban kalubalen da ba ta taba gani ba”.
Wannan takardar bayani kan tsaro, daftari ne da Japan kan fitar a hukumance domin bayyana yanayi da manufofinta na tsaro, kuma abu ne da ake gani a matsayin alkiblar manufar Japan kan tsaro. A shekarar 1970, gwamnatin Japan ta fitar da wannan takardar bayani ta tsaro a karon farko, sannan ta ci gaba da fitarwa a kowace shekara daga shekarar 1976.
Sabuwar takardar bayanin, ta kara maimaita abun da Japan ta dade tana ikirari wato “Barazanar Kasar Sin”, kana ta hada shi da sabon nazarin da ta yi kan yanayin tsaro. Takardar ta ambato burin zuba kimanin kudin Yen triliyan 43 kan tsaro a cikin shekaru 5, zuwa shekarar 2027, domin raya abun da ta kira “karfin mayar da martani” da “karfafa karfin tsaro daga tushe” da “neman fahimta” game da wadannan manufofi.
Wasu masharhanta sun yi imanin cewa, wannan kasafi da Japan ta yi kan tsaro, na bayyana yunkurinta na neman kare burinta na fadada karfinta na soji ta hanyar wuce gona da iri wajen bayyana cewa tana fuskantar barazana, domin soke tanadin kundin tsarin mulkinta da ya ayyana “kaucewa shiga yaki” da farfado da burinta na samun karfin soji. (Fa’iza Mustapha)