Mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya ce manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su samar da mafita idan dukkan hanyoyin da aka bi a siyasance ba su yi tasiri ba bayan juyin mulki a Nijar.
“Matakin soji zai zama na karshe da za a dauka,” kamar yadda ya bayyana.
- Cire Tallafin Fetur: Gwamnatin Zamfara Ta Amince Da Raba Kayan Abinci Don Tallafawa
- Me Ya Haifar Da Koma Bayan Ababen More Rayuwa A Kasar Amurka?
Manyan hafsoshin tsaron kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma sun tattauna a Abuja domin nemo hanyoyin da za a bi wajen shawo kan sojojin da suka yi juyin mulkin, inda suka hambarrar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a makon da ya gabata.
Manyan hafsoshin tsaron Ghana da Nijeriya da Benin da Togo da Saliyo da Laberiya da Gambiya da Cote D’Ivoire da Cape Verde ne suka halarci taron.
Sai dai takwarorinsu na Mali, da Nijar, da Guinea Bissau, da Burkina Faso, da Guinea ba su halarta ba sakamakon dakatar da su da ECOWAS ta yi daga kungiyar saboda juyin mulkin da suka jagoranta a kasashensu.
Manyan hafsoshin tsaron za su gabatar da matakin da suka cimma ga shugaban kungiyar Bola Tinubu a ranar Juma’a.
Daga nan ne shugaban kungiyar zai yanke shawara kan mataki na gaba da za a dauka kan sojojin karƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya ayyana kan sa a matsayin shugaban Nijar.