A jiya Laraba ne aka bude sanannen taron harkokin sufurin jiragen sama na duniya a Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin, inda ya samu halarcin kwararrun masana’antar sufurin jiragen sama fiye da 1,000 daga sassan duniya.
Paul Chan, sakataren kudi na gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ya bayyana a yayin bikin bude taron cewa, akwai haske a makomar Hong Kong a matsayinsa na cibiyar zirga-zirgar jiragen sama, tare da kyakkyawar yanayin hada-hadar kasuwancin na babbar yankin Guangdong-Hong Kong-Macao (GBA) da ɗimbin ci gaban ababen more rayuwa.
Taron na kwanaki biyu da HKIA da ƙungiyar sufurin jiragen sama ta duniya suka karbi bakunci, ya samu halarcin shugabannin masana’antu don musayar ra’ayi kan batutuwan da suka haɗa da sabbin damammakin zirga-zirgar jiragen sama da jigilar kaya a cikin GBA, da sabbin hanyoyin fasaha a cikin masana’antar sufurin jiragen sama, da sauransu. (Mai fassara: Yahaya)