Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta bayyana Muhammad Abacha, dan gidan tsohon shugaban kasar nan na mulkin soja, Sani Abacha,a matsayin wanda ya lashe zaben fid-da gwani na jam’iyyar PDP.
Tun bayan kammala zaben fid-da gwani a Kwanakin baya dai cece-kuce ya barke tsakanin tsagi biyu a cikin jam’iyyar inda bangaren Shehu Wada Sagagi ya gudanar da nasa zaben fid-da gwanin sannan shima bangaren Aminu Wali ya gudanar da nasa.
Bayan kammala zabubbukan dai Muhammad Abacha ne aka bayyana ya samu nasara daga bangaren Shehu Wada Sagagi ya yinda Sadiq Wali, aka bayyana shi shima a matsayin wanda ya samu nasara daga bangaren mahaifinsa, Aminu Wali, wanda tsohon minista ne.
Sai dai a jiya Alhamis, kwamishinan hukumar zabe ta jihar Kano, Farfesa Risqua Shehu, ya bayyana wa manema labarai cewa Muhammad Abacha ne wanda hukumar ta sani, wanda bangaren Shehu Wada Sagagi ya zaba.
“A lokacin da aka gudanar da zaben fid-da gwani a jam’iyyar PDP Shehu Wada Sagagi ne halastaccen shugaban jam’iyyar a doka Kuma shine zaben da muka tura wakilan mu domin su saka ido.
Ya ci gaba da cewa “Duk da cewa zaben fid-da gwani abu ne wanda ya shafi jam’iyya amma zaben da Shehu Wada Sagagi ya gudanar shine wanda muka sani”
Ya Kara da cewa wasu mutane sunzo daga ofishin uwar jam’iyya daga Abuja inda suka ce sune waÉ—anda jam’iyya ta turo su gudanar da zaben amma ba suzo da adireshin inda za’ayi zaben ba, sai dai Shehu Wada Sagagi ya kawo mana takarda shima tare da adireshin inda za’a gudanar da zaben, hakan yasa muka tura wakilan mu domin sanya ido akan yadda za’a gudanar da zaben.