Mahukuntan sojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar an ruwaito cewa, sun rufe sararin saman kasar biyo bayan cikar wa’adi da barazanar da shugabanin kungiyar ECOWAS suka yi, na yin amfani da karfin soji matsawar sojin da suka yi juyin mulkin ba su dawo da shugaban kasar, Mohamed Bazoum, akan Karagarsa ba zuwa ranar 6 ga watan Agusta ba.
Sojin sun rufe sararin sama kasar ne, bayan cikar wa’adin da kungiyar ta ba su.
- ECOWAS Za Ta Gudanar Da Taron Ƙoli A Abuja Kan Batun Juyin Mulki A Nijar
- Burkina Faso Da Mali Za Su Tura Tawagar Sojoji Zuwa Nijar
Jagoran da ya jagoranci juyin mulkin, Janar Abdourahmane Tchiani, ya ki sauka a makon da ya wuce bayan sun kifar da gwamnatin farar hula ta Bazoum a ranar 26 na watan Yulin 2023.
A cikin sanarwar da sojin suka fitar sun yi ikirarin cewa, duk wani yunkirin da aka yi na karya dokar ta su ta rufe sararin saman kasar, za su mayar da martani.
Rahotanni a ranar Litinin sun bayyana cewa, babu alamun wani Jirgin sama da ke yin shawagi a sararin saman kasar ta Nijar.