Saudiyya ta jagoranci zaman yin sulhu tsakanin Rasha da Ukraine da suka shafe sama da shekara guda suna gwabza yaki a tsakaninsu.
Sai dai Rasha ta ce yin sulhu tsakaninta da Ukraine abu ne mai yiwuwa, to amma fa bisa sharadin dole sai dakarun Ukraine din sun dakatar da dukkanin hare-haren da suke kai wa sojojinta.
Baya ga sharadin dakatar da kai wa dakarunta farmaki, Rasha ta kuma bukaci Ukraine da ta hakura da dukkanin yankunan da a yanzu haka sojojinta suka mamaye a tsawon fiye da shekara guda da suka shafe suna fafatawa.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Mutunta Ikonta Na Teku
- Sojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Rufe Sararin Saman Kasar
Rasha ta bayyana matsayin nata ne sa’o’i kadan bayan taron tattaunawar sulhu na kwanaki biyu kan yakin Ukraine, da Saudiyya ta karbi bakunci, da ya samu halartar jami’an difllomasiya daga kasashe 40, wanda ba a gayyaci Rashan ba.
Wani babban jami’in diflomasiyar Ukraine, ya ce taron na Saudiyya ya samu nasara, yayin da Rasha ta yi watsi da ikrarin.
A baya-bayan nan ne dai Ukraine ta sanar da cewa Rasha ta sako mata sojoji 22 yayin musayar fursunoni na baya-bayan nan da suka yi, sai dai bangaren Rasha bai yi karin bayani kan batun ba, don haka ba a san adadin nata sojojin da Ukraine ta saki ba.