Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa NIS, Caroline WuraOla Adepoju, ta kai ziyara kan iyaka ta Illela da ke Jihar Sokoto domin tabbatar da bin doka da oda da gwamnatin tarayya ta bayar na rufe kan iyakokin kasar da jamhuriyar Nijar na wucin gadi.
Gwamnatin ta bayar da umurnin ne sakamakon rashin jituwar siyasa da kasashen biyu ke fuskanta a tsakaninsu sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a Nijar.
Kwanturola Adepoju ta kai ziyarar ne don tabbatar da bin umurnin gwamnatin tarayya da kuma karfafa alakar aiki da takwarorin hukumar da ke aiki kan iyakar tare da bayar da bayanan sirri a tsakaninsu.
A yayin ziyarar da ta kai a ranar Laraba 9 ga watan Agustan 2023, mukaddashiyar CGI ta bayyana gamsuwarta da yadda Jami’anta suka bi umurnin gwamnatin tarayya akan iyakar da ke Illela. Ta kuma mika godiyarta ga jami’an bisa jajircewar da suka yi wajen bin umarnin rufewar.
Mukaddashiyar CGI Adepoju ta yi amfani da wannan dama wajen sake nanata umarninta na farko ga daukacin Kwanturolan Hukumomin Jihohin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar, wajen tabbatar da rufe iyakokin Jihohin da suke.
Da take jawabi ga jami’an, CGI Adepoju, ta bayyana aniyarta na sake inganta jin dadi da walwalar jami’anta kan irin kalubalen da suke fuskanta musamman yadda cire tallafin man fetur ya sanya rayuwa ta yi tsada a fadin Nijeriya.