Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bukaci bangaren Philippines, da ya gaggauta tattaunawa da tsagin Sin, don tabbatar da an kawo karshen takaddamar da ta kunno kai a tekun kudancin kasar Sin.
A ranaikun Alhamis da Juma’a, Wang, ya tattauna da jami’an gwamnatocin kasashen Singapore da Malaysia, game da halin da ake ciki a yankin tekun kudancin Sin, ya kuma jaddada matsayar Sin, yayin ziyarar aiki da ya kai kasashen 2.
A cewar sa, cikin shekarun baya bayan nan, an cimma daidaito a yanayin yankin tekun kudancin Sin, an kuma samar da kyakkyawan yanayi na bunkasuwar kasashen yankin, bisa hadin gwiwar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN.
Wang ya kara da cewa, Amurka da wasu karin sassa, sun ci gaba da yamutsa hazo, bayan sun lura cewa ba wasu alamu na barkewar rikici a yankin. Ya ce sassan sun yi amfani da batun tsibirin Ren’ai Jiao domin tada tarzoma, da haifar da tashin hankali tsakanin Sin da Philippines, sun yi ta rura wutar fito na fito, da gurgunta yanayin zaman lafiya da lumana a yankin tekun kudancin Sin, da nufin cimma muradun siyasa da suka tsara.
Daga nan sai ministan harkokin wajen kasar ta Sin, ya bayyana fatan sa, na ganin kasashen yankin sun kiyaye matsayin su, da adawa da duk wasu dake fatan ganin sun haifar da rikici, su kuma aiwatar da matakai na kashin kan su, wadanda za su kai ga cimma yanayin zaman lafiya da daidaito a tekun kudancin kasar Sin. (Saminu Alhassan)