Jihar Gombe ta samu nasara a kididdigar kasafin kudi na 2023 wadda BudgetIT ta wallafa, wacce cibiya ce da ta shahara wajen bin diddigin manufofin kudi a Nijeriya.
Jihar ta zo matsayi na 6 daga cikin jihohi 36, inda ta samu maki 74 bisa 100.
Rahoton ya yaba da irin nasarorin da Jihar Gombe ta samu a fannoni daban-daban da suka hada da nuna gaskiya a harkokin kasafi da kashe-kashen kudi, da nuna aminci da sahihanci a rahoton gudanar da kasafin kudi ta shafin yanar gizon jihar.
Wani babban abin lura ma shine tsarin kasafin kudin jihar na matsakaicin zango (MTEF), wanda aka bayyana shi a matsayin cikakke kuma mai kyakkywan tsari.
Rahoton ya tabbatar da cewa kasafin kudin Jihar Gombe da aka amince da shi ya cika sharuda da dama, yayin da harkokin kashe-kashen kudi na yanar gizon jihar ya kasance a saukake ga mai bukatar bincike da nazari.
Bugu da kari, Jihar Gombe ta kasance ta 7 a Nijeriya, yayin da a yankin Arewa maso gabas kuwa ta yi fintinkau a fannin gudanar da ayyuka cikin gaskiya da rikon amana, matsayin da ta samu daga cibiyar kula da harkokin kudi ta ƙasa (CETIW).
Farfesa kuma mai bincike da nazari a fannoni daban-daban, wanda kuma shi ne babban daraktan bincike da tattara bayanai a gidan gwamnati, Dr. Mu’azu Shehu ya bayyana cewa, bisa la’akari da yadda yake sanya ido sosai kan ayyukan gwamnati da kuma kimanta ci gaban kasa, Jihar Gombe ta yi fintinkau a fannin tafiyar da harkokin kudi cikin gaskiya da adalci da ɗorewar ayyuka na gari.
Ya yi nuni da cewa, shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da shugabanci nagari da kuma tabbatar da gaskiya, tare da sanya Jihar Gombe a matsayin Jihar da samu shugabacin mai cike da riƙon amana ba tare da nuna wariya ba.
“Gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya tana ci gaba da jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana a kasafin kudi, wanda hakan ya sa Jihar Gombe ta samu karramawa a matakin kasa da na kasa da kasa. Musamman ma, a kwanan nan jihar ta samu lambar yabo na Bankin Duniya a Fannin tabbatar da gaskiya, adalci da dorewarsu wato (SFTAS) a fannoni dandan daban, hakan wata shaida ce dake nuna irin jajircewar gwamnatin Inuwa wajen kulawa da dukiyar talakawa.”