Shugaban jami’yyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya bukaci ‘yan majalisar dokokin APC 14 na jihar Kano da su mara wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf domin ci gaban jihar.Â
Yusuf dai, ya kasance dan jami’yyar adawa ta NNPP wanda kuma akwai zazzafar adawar siyasar a tsakaninsa da Ganduje tsohon gwamnan jihar Kano.
- Cinikin Maguire daga Manchester United Zuwa West Ham Ya Lalace
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Ango Da Amarya A Filato
Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ‘yan majalisar dokokin jihar suka je sakatariyar APC ta kasa da ke Abuja domin ta ya shi murnar zama shugaban APC na kasa.
Ya yi nuni da cewa, mara wa gwamnan jami’yyar adawa, ba wai hakan na nuna cewa sun bar dangantakarsu a matsayin ya’yan APC ba ne.
Ya kara cewa, gwamnan jihar mai ci daga wata jami’yyar ya fito, amma ina son ku sani cewa, ribar siyasa, shi ne bunkasa rayuwar al’umma saboda haka, ina ba ku shawara cewa, duk da banbancin siyasa, ku mara wa gwamnatin jihar mai ci baya don a ciyar da jihar gaba.
Kazalika Ganduje ya ce, mara wa gwamnatin ta Yusuf baya, ba wai hakan zai dakatar da ku daga ci gaba da rike matsayinku na ‘yan majalisar dokokin jihar Kano ba ne har ila yau, yin hakan ba zai dakatar da mu daga yin aiki a tare domin mu sake kafa gwamnatin APC a jihar ba ne.
A cewarsa, abin da ke da muhimmanci ga al’ummar jihar, shi ne a samar musu da romon dimokuradiyya.
Bugu da kari, ya ce ina baku tabbacin cewa, za mu ba ku dukkan goyon bayan domin mu kara samun karin wasu ‘yan majalisar dokoki a jihar da kuma sake samun kafa wata sabuwar gwamnatin APC a Kano.