Gwamnatin Tarayya ta ce za ta janye tuhumar mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da ta shigar kan dakataccen gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Gowdin Emiefle, da kuma shigar da wasu sabbin tuhume-tuhume a kansa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.
A ranar 25 ga watan Yuli ne, wani alkali ya bayar da belin Emefiele kan Naira miliyan 20 kan wasu zarge-zarge guda biyu da ake yi masa, da ya hada da zargin mallakar makamai, inda ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali a Ikoyi, har sai ya cika sharudan belin.
- Juyin Mulki: Hafsoshin Sojin ECOWAS Za Su Cimma Matsaya A Kan Nijar
- Yadda Kasar Sin Ke Hada Hannun Kasa Da Kasa Wajen Inganta Muhallin Duniyarmu Ta Bai Daya
Sai dai hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta sake kama shi bayan wani artabu da jami’an gidan yari.
A ranar Talata, daraktan shigar da kara na ma’aikatar shari’a, Mohammed Bakodo, ya fada wa mai shari’a Nicholas Oweibo cewa ya ce za a yi wa Emefiele sabbin tuhume-tuhume ne bayan karin bincike da aka gudanar.
Sai dai lauyan da ke kare wanda ake kara, Joseph Dauda, ya yi adawa da hakan, inda ya kalubanci cewa gwamnati ta ki bin umarnin kotu na bukatar sakin Emefiele.
Da yake magana da manema labarai, Abubakar ya ce an shigar da sabbin tuhume-tuhumen ne a wata Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Daya daga cikin sabbin tuhume-tuhumen na zargin Emefiele da bai wa kansa haramtattun damarmaki ta haramtacciyar hanya.