A yau Laraba 16 a watan Agusta masu masaukin baki kasar Australia zasu fafata da kasar Ingila a wasan gab da na kusa da na karshe na kofin Duniya na mata.
Kadan daga cikin abubuwan da ya kamata ku akan wasan sune; kasashen biyu sun buga wasanni uku a tsakaninsu inda kasar Ingila ta samu nasara a wasanni biyu yayinda kuma Australia ta samu nasara sau daya.
- Mu Muka Harbo Jirgin Sojojin Nijeriya – Kasurgumin Dan Bindiga
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Yi Wa Emefiele Sabbin Tuhume-Tuhume
Wannan shine karo na farko da kasar Australia ta kawo matsayin Semi Final a gasar cin Kofin Duniya na mata.
Kasar Ingila kuwa sun taba karewa a matsayi na uku.
Duk wanda ya samu nasarar tsallakewa mataki na gaba zai buga wasan karshe da kasar Sifaniya.