An kaddamar da baje kolin mutum-mutumin inji na duniya na shekarar 2023 a birnin Beijing jiya, taken baje kolin na bana shi ne “bude kofa da yin kirkire-kirkire don samun kyakkyawar makoma tare”, burinsa shi ne baje kolin fasahohin zamani da sabbin nasarorin da aka cimma a fannin fasahar mutum-mutumin inji a duniya, da gina dandalin yin musayar fasahohi da hadin gwiwa da more nasara tare a wannan fanni.
Rahotanni na cewa, yayin bikin baje kolin na bana kamfanonin fasahohin robot na Sin da kasashen waje 160 sun gwada kayayyakinsu kimanin 600 ciki har da sabbin fasahohi zamani 60 karo na farko ne da aka baje kolinsu a gaban duk duniya.
Wakilan hukumomin kasa da kasa, da shehunan malamai, da masana, da ’yan kasuwa da yawansu ya zarce 320 sun halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu, wadanda suka gabatar da rahotanni da yin shawarwari a fannonin bude kofa da yin hadin gwiwa, da raya fasahohin mutum-mutumin inji, da maida hankali ga yadda ake amfani da mutum-mutumin inji da kuma sauran muhimman batutuwa.
A yayin taron, za a gabatar da rahoton raya fasahohi da sha’anin mutum-mutumin inji na kasar Sin na shekarar 2023, sabbin munimman fasahohin zamani 10 da za su bullo a tsakanin shekarar 2023 da ta 2024, da kuma kundin makalolin fasahohin mutum-mutumin inji na duniya na shekarar 2023 da sauransu. (Zainab Zhang)