Masu karatu Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Har yanzu dai muna nan a cikin darasinmu na budi, cikar ni’ima da sauran abubuwa na girma da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) kamar yadda muke waiwaye a cikin Suratul Fat’hi.
Allah ya ce “Hakika mu muka aiko ka mai shaidawa (ga al’ummarka), mai bushara gare ta, mai gargadi gare ta… (har zuwa karshen ayar”. Allah ya kirga kyawawan abubuwa ga Annabi (SAW) da kebance-kebacen da ya yi masa na cewa Annabi zai yi shaida ga al’ummarsa da kuma kansa; da cewa ya isar musu (al’ummarsa) da aike. Kila kuwa aka ce mai shaidawa ne gare su da Tauhidi, Annabi zai yi shaida ga al’ummarsa da suka ce La ila ha illallahu Muhammadur Rasulullah (SAW) a matsayin Musulmi ne. Annabi mai bushara ne ga al’ummarsa da samun ladan Ubangiji, kila aka ce Manzon Allah mai bushara ne ga al’ummarsa da gafara. Mai gargadi ne kuma ga makiyansa da azaba, kila kuma aka ce mai gargadi ne a kan kar al’ummarsa ta bace. Wanda kyakkyawa ta rigaya da shi daga Allah sai ya yi imani da Allah tun da Manzon Allah ya yi masa gargadi. Sai kuma ya yi imani da Manzon Allah (SAW).
Allah ya ce wa al’ummar Annabi su girmama shi (SAW), mutum ya girmama Manzon Allah domin ba kawai na ganin dama ba ne hakan, a’a, Allah ne ya ce ka girmama shi. Kila ma’anar girmama shi kuma, ana kira ne ga al’ummarsa su taimake shi. Kila kuma abin da ake nufi shi ne mutane su kai matuka wajen girmama shi, to ina wadanda idan suka ga an yi wani abu na girmama Manzon Allah (SAW) sai su rika cewa ana yin abin da Allah bai dora wa mutum ba, an ki barci, an barnata kudi kaza da kaza? Yau dai ya kai matukar girmama Annabi (SAW) a ga mutum Dattijo ya hakura da barci, ya kashe kudinsa ya shafe dare cur a zaune saboda Manzon Allah (SAW). Ya fitar da kudinsa ya sayi dabba ko saniya ko rago ko wani abu ya ce ya yanka wa Manzon Allah (SAW), ai ya girmama ko? Ko ya dafa abinci, ko ya je Madina ya ziyarci Manzon Allah. Ba wai ya je Makka don yin Umura ko Aikin Hajji ba daga nan ya wuce, a’a, ya tashi musamman ya tafi Madina don ya ziyarci Manzon Allah (SAW), ka ga wannan ai ya girmama Manzon Allah saboda Allah ya ce mu kai matuka wajen girmama shi. Amma yanzu wannan zai yi daidai da wanda zai ce ko an je Makka kar a ziyarci Manzon Allah? Ga shi nan za ka ga ana ta yin wa’azin hakan a Minna. Yanzu mai fadar wannan duk irin abin da zai fada na cewa shi ma Masoyin Manzon Allah (SAW) ai shi kansa ya san karya yake yi. Yanzu ko Babanka ne a Saudiyya, ka je Makka ka yi Hajji ko Umura amma ka ki zuwa ka ziyarce shi ka gaishe shi, me ka yi kenan? Ai ka zama dan baya. Baban naka ba zai ji dadi ba. Ballantana kuma a ce ba Babanka ba ne, Annabinka ne (SAW) wanda Allah ya ce mu kai matuka wajen girmama shi.
Wani sashen Malamai kuma (kila Abdullahi bin Abbas) ya karanta karatun da “wa yu abbizuhu”, maimakon “wa yu azziruhu), wato ayar tana nufin a girmama Manzon Allah, a kambama shi, a daukaka shi, gari gabadaya kowa ya yi kokari idan za a yi wani abu na girmama Manzon Allah (SAW) kowa ya yi iya karfinsa. Abin da ba a tabawa a gidanka rannan a fitar da shi a yi amfani da shi. Mun ga Malamanmu irin su Shehu Malam Murtala Gusau, ko cokali ya saya a Madinar Manzon Allah (SAW) to wanna n cokalin mai girma ne a wurinsa. Idan ka batar zai yi fada, ya ce idan ka batar da cokali dubu na gida ba komai, amma wancan a Madinar Manzon Allah (SAW) na sayo shi. To yanzu kai dansa ko almajirinsa za ka yi wasa da Annabi? To amma ga wani can, ba wai cokali ko darduma da aka saya a garin Annabin yake girmamawa ba, a’a, Annabin ma gabadaya (SAW) ya ce ba sai ka ziyarce shi ba!
A karshen ayar kuma Allah ya ce a yi masa tasbihi safe da yamma, amma kuma sai ya hade abin da abubuwa na girmama Manzon Allah (SAW) don ya kara nuna mana girman Annabi. Wannan ishara ce da gargadi ga wadanda idan an girmama Manzon Allah (SAW) sai su ce an yi shirka, an kai Manzon Allah inda Allah bai kai shi ba (a uzu billahi), wani wuri ne wannan? A duk karatun duniya, ka dauko Alkur’ani kaf za ka ji irin matsayin da Allah ya kai Manzon Allah (SAW). Allah ya kai shi “kaba kausaini au adna”, ba malamin duniya tun daga Sahabbai zuwa yau da ya iya fassara “au adna”. To ka taba jin wanda ya kai wannan matsayin? Alkur’ani shi ne duk ya kakkai Manzon Allah (SAW) inda ake fada ba wani mutum ba.
Malam Dan Ada’u ya ce an tara wa Manzon Allah (SAW) ni’imomi a cikin wannan Sura (ta Fat’hi) mabanbanta, cewa Allah ya yi masa budi mabayyani, da cewa Allah ya amsa masa duk abin da ya roka (na cikin addininsa da al’ummarsa). Allah ya gafarta masa, ita gafarar nan tana daga sanarwar Allah yana son sa (duk mutumin da idan ya yi ma laifi ba ka ganin laifin, a kawo kararsa ya yi kaza da kaza; sai ka ce to sai me? ai ka san kana son sa kuma kowa zai shaida hakan).
Ita kuwa cika masa ni’ima da Allah ya yi, tana sanar da mu cewa Allah ya zabe shi kenan. Shiryarwarsa kuwa tana sanar da mu cewa Allah ya jibince shi, shi ya sa ya shiryar da shi. Gafara kuma ita ce kubutar da shi daga duk wani abu na laifi da aibi. Cikar ni’ima kuma ita ce an kai Manzon Allah daraja ta karshe har an kai shi matsayin “Wasila” da “Fadhila” (SAW). Shiriya ita ce kiransa (SAW) da aka yi ya je ya gana da Ubangijinsa, ba wani Annabi da ya samu wannan.
Sharifi Ja’afaru Dan Muhammadu (Sadik) RTA ya ce, yana daga cikar ni’ima da Allah ya yi wa Annabi Muhammadu (SAW) ya sanya shi a matsayin “Habibahu”, wato Babban Masoyinsa. Ya ishi girmamawa ga Manzon Allah da Allah ya rike shi Masoyi. Allah ya rantse da rayuwarsa (mun yi wannan karatun a baya). Allah ya soke shari’o’in Annabawa duka da Shari’ar Manzon Allah (SAW). Allah ya yi Mi’iraji da shi, wato ya hawar da shi zuwa bigire madaukaki da ba wani abin Halitta Dan Adam ko Mala’ika da ya taba zuwa. Babu wata halitta da ta taba zuwa nan. Allah ya kiyaye shi a cikin tafiyar (ta Mi’iraji), har ya zamo idonsa bai karkace ba kuma bai yi shan zara ba. Allah ya aiko shi zuwa jar fata da bakar fata. Allah ya halatta masa da al’ummarsa ganimomin yaki. Allah ya sanya shi mai yin ceto ranar tashin kiyama kumwanda za a karbi ceton nasa. Allah ya sanya shi a matsayin shugaban ‘ya’yan Adam kaf. Allah ya hada ambatonsa da ambaton Allah. Allah ya sanya yardar Manzon Allah ta zama yardar Allah ce. Allah ya sanya shi a matsayin dayan rukunin Tauhidi, wato in dai ka ce “La ila ha illal lahu” ba ka ce “Muhammadur rasulullahi” ba, Musuluncinka bai tabbata ba. Kafiri idan ya zo shiga Musulunci aka ce ya fadi “La ila ha illal lahu…” ya fada, aka zo “Muhammadur rasulullah” sai ya ce a’a, ai cewa aka yi a kadaita Allah don haka ba sai ya fada ba, idan ya yi haka, shin ya musulunta? Ai Musuluncinsa bai inganta ba.