Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce, jarin kai tsaye da kasar ta zuba a ketare, ya ci gaba da bunkasa a watanni 7 na farkon bana, inda ya karu da kaso 18.1, zuwa yuan biliyan 500.9
Kakakin ma’aikatar Shu Jueting ta bayyana jiya yayin wani taron manema labarai cewa, idan aka kwatanta adadin a kudin dala, jarin a cikin wadancan watanni ya kai dala biliyan 71.93, wanda ya nuna karuwar kaso 10.6 a kowacce shekara.
Daga watan Junairu zuwa Yuli, jarin da ba na kudi ba da Sin ta zuba a kasashen dake kan hanyar Ziri Daya da Hanya Daya, ya kai dala biliyan 13.69, wanda ya karu da kaso 15.3 daga shekara 1 da ta gabata, kuma ya dauki kaso 19 na jimilar jarin kai tsaye na kasar Sin a ketare. (Fa’iza Mustapha)