A kokarinta wajen shawo kan matsalolin karancin abinci ga jama’a, ranar Juma’a Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da tallafin kayan abinci sama da ton 360 ga gwamnatin jihar Yobe, domin raba su ga masu karamin karfi da nakasassu a fadin jihar.
Da yake jagorantar rabon kayan abincin, Engr. Abubakar D. Aliyu, ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya aiko shi domin ya wakilce shi zuwa jihar don ya mika kayan abincin ga gwamnatin Yobe kuma ya shaida fara raba shi ga al’uma.
- Rahoton INEC Ya Nuna Machina Ne Dan Takarar Sanatan APC A Yobe Ta Arewa
- An Fafata Da Lawan A Zaben Fidda Gwanin Sanatocin Yobe – Shugaban APC
Ministan ya kara da cewa shugaba Buhari ya bayar da umurnin wajen fitar da kayyayakin abincin daga rumbuna na musamman wanda gwamnatin tarayya ke tanadin kayan abinci da masarufi domin tallafa wa ‘yan gudun hijira da masu karamin karfi wajen ragewa jama’a radadin kuncin rayuwa da tsadar kayan abincin.
Da yake karbar kayan abincin, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda mataimakin shi ya wakilce shi a taron, Alhaji Idi Barde Gubana, ya fara da mika godiyarsa ga gwamnati da al’umar jihar Yobe baki daya tare da yaba wa kokarin gwamnatin tarayya bisa hangen nesa da jinkan da ta nuna wajen tallata wa al’umar jihar, wadan da suka fuskanci nau’uka daban-daban na ibtila’in rayuwa.
Gwamna Buni ya bai wa gwamnatin tarayya tabbacin mika kayan tallafin ga jama’a bisa kamar yadda ta tsara- musamman iyalai maras karfi da nakasassu da ke fadin jihar.
Kayan abincin sun kunshi ton 210 na masara (kimanin buhuna 4200) masu nauyin 50kg; da ton 60 na gero (kimanin buhu 1, 200) masu nauyin 50kg; sai ton 60 na dawa (buhuna 1,200) masu nauyin 50kg, hadi da ton 30 na garri (buhuna1, 200) masu nauyin 50kg.