Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake aduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na ado da kwalliya.
Kafur wani nau’in abu ne wanda yake zuwa kala kala amma mafi akasarinsa fari akafi sani sannan kuma yana zuwa manya da kanana lalle kafir yana da amfani so sai a gida harma lokacin damuna saboda gyaran gida sannan yana hana zuwan kwari sannan kuma yana dauke warin ruma na kaya ko gida harma bayan gida yana hana shi wari da zuwa kwari kamarsu gyangyaso sannan kuma yanasa kamshi a waje a duk inda aka sashi.
Ana amfani da kafur cikin kaya wato cikin durowa da cikin akwati idan uwargida ta samu wannan kafur din zaki zuzzuba shi, idan cikin cikin durawar kaya ne zaki sashi a wuri wuri haka da gefe da gefe sai ki jera kayanki idan kuma suna jere zaki sa su matsi matsi ki bada kwana biyu idan kika dakko kayanki zaki ji baya warin ruma ko kuma wani kwaro ya shiga ya ci miki kaya kinsan akwai kwaron dake cin kaya kafur yana maganinsa.
Sannan zaki iya sa kafur a bayan gida zaki sa shi matsi tatsi da kuma wajen wucewar ruwa da kuma wajan cikin sink da kan tagar bayan gida saboda duk zai cire miki wani wari na bayan gida da wasu kwari.
Sannan zaki iya dan jajjefa shi cikin gidanki matsi-matsi haka saboda yara kidan babboye shi kamshinsa yana tashi.