Assalamualaikum jama’a barkanmu da sake saduwa a wannan satin inda za mu yi magana akan yadda ake sana’ar kwalliya. Sanaar kwalliya sana’a ce da ke da dimbin riba don ya samu karbuwa sosai a gun mata.mace dai sai da ado.
Wannan sana’ar idan ki ka fara ta sana’a ce da ba ta bukatar shago amma in da halin bude shago za ta karbu sosai saboda samun jama’a.
Idan kika saya kit din wato kayan kwalliyan don hawa hawa ne.kuma kowanne occasion da nashi irin kwalliyar.
Akwai harsh makeup akwai kuma simple makeup. yawanci simple makeup din nan za ki iya yi wa wata makeup ko chaje ta Naira15000 kuma harsh makeup kuma irin wadda ake wa amare na biki ko suna ko wani serious occasion.
Abubuwan da kike bukata yayin fara wannan sana’ar.
1.Contour/Bronzer 2. Foundation 3. Setting powder 4. Mascara 5. Eyeliner/Gel liner
6. Jagira 7. Eye shadow 8. Concealer 9. Eye lashes 10. Brow Gel. 11. Highlighter
12.wipes. 13 shimmer 14. Beauty blender sponge 15. Blusher 16. Moisturizer/Primer/Make up setting spray 17. Brushes.
Ga yadda ake amfani da su daya bayan daya.
1. Wipes:wannan ya na daga cikin kayan kwalliya wanda ake amfani da shi wurin goge fuska.
2. Foundation: Wannan powder ce mai ruwa, ana shafa ta kafin a shafa powder, tana kara ma kwalliya kyau sosai, ta na zuwa nau’i kala-kala, wata mai ruwa, wata mai maiko.
3. Setting powder:wannan shi ne powder da ake shafawa bayan kin shafa foundation, amfanin ta shi ne yana sa fuska ta yi Kuwait-kuwait ta yi kyau, sannan ta na rage duk wani gumi da maiko na foundation.
Wannan powder ta na zuwa a daskare a bushe ita ake cema cake powder ko kuma ta zo a gari, akwai certain contact powder da ake highlight setting da ita da kuma contour