A yau ne, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi zuwa birnin Johannesburg don halartar taron shugabannin kasashen BRICS karo na 15 da kai ziyarar aiki a kasar Afirka ta Kudu, ya gabatar da bayani mai taken “Sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu da sada zumunta a tsakaninsu zuwa sabon matsayi” wanda aka wallafa a jaridun The Star, da Cape Times, da The Mercury, da shafin internet ta Independent Online.
A cikin bayanin, Xi Jinping ya yabawa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu wadda ta shiga lokaci mai kyau, da kawo wa duniya tasiri mai muhimmanci.
Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai tare da kasashen BRICS da bin tunanin BRICS na bude kofa da amincewa da bambance-bambance da hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna, kana sun cimma daidaito kan manyan batutuwa, da yada tsarin diplomasiyya mai ‘yanci, da tabbatar da adalci a duniya, da sa kaimi ga kasa da kasa da su mai da hankali kan batun samun bunkasuwa, da sa kaimi na ganin tsarin hadin gwiwa na BRICS ya taka muhimmiyar rawa wajen tsarin tafiyar da harkokin duniya.
Bana shakaru 10 ke nan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da manufofi game da nahiyar Afirka wato nuna adalci da yin imani da juna da raya hadin gwiwa da kuma zama hakikanin aboki.
A cikin wadannan shekaru 10, Sin da Afirka sun yi kokari tare wajen neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, da kammala manyan ayyukan gine-gine kamar cibiyar tinkarar cututtuka ta Afirka da sauransu. Xi Jinping ya bayyana fatansa na hada kai tare da shugabannin Afirka wajen sa kaimi ga daukar matakai masu yakini da amfani da samun bunkasuwa mai dorewa a nahiyar Afirka, tare da fatan kasashen Afirka da kungiyar AU za su kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa da yankuna. (Zainab)