Jam’iyyar PRP ta bukaci kungiyar ECOWAS da ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen yunkurin tunkarar gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa Alhaji Falalu Bello ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
“Jam’iyyar PRP ta na fatan cewa Nijeriya da ECOWAS za su warware matsalar da ke tattare da su cikin lumana ta hanyar tattaunawa ba tare da zubar da jini ba.
“Muna kira da babbar murya ga Shugaba Bola Tinubu a matsayinsa na Shugaban ECOWAS na yanzu, da ya himmatu wajen neman tattaunawa da diflomasiyya wajen warware matsalolin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar ba tare da daukar duk wani mataki da zai kai ga gwabza yaki ba.
“Muna kira ga Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, da suka hada da rashin tsaro, matsanancin talauci da rashin aikin yi ga matasa da sauransu.” inji Falalu