Rahotanni daga kasar Japan na cewa, gwamnatin Japan za ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya daga tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi zuwa cikin tekun da karfe 1 na yammacin ranar 24 ga watan Agusta. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin ba ta fatan ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2023 za ta zama ranar kawo barazana ga yanayin teku. Idan Japan ba ta canja ra’ayinta ba, tilas ne ta dauki alhakin duk abin da zai biyo baya a tarihi.
Ban da wannan kuma, yayin da yake karin haske kan takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wa jami’an kasar Sin ba bisa ka’ida ba bisa la’akari da batutuwan da suka shafi yankin Tibet, Wang Wenbin ya ce, Amurka ta yi watsi da gaskiyar lamarin, ta sanya takunkumi ba bisa ka’ida ba kan jami’an kasar Sin bisa la’akari da batutuwan da suka shafi yankin Tibet, ta tsoma baki a harkokin cikin gidan Sin, da yin mummunar illa ga moriyar kasar Sin, kuma hakan ya keta ka’idojin dangantakar kasa da kasa matuka.
A dangane da sanarwar da kungiyar EU ta fitar na cewa, dukkan kasashe mambobin kungiyar za su shiga cikin kudurin Amurka na hana gwaje-gwajen makami mai linzami, Wang Wenbin ya ce kudurin na Amurka bai magance hakikanin barazanar tsaro a sararin samaniya ba, kuma ba ya daidaita matsalar da abin ya shafa ko kuma tushen wannan batu.
Bugu da kari, Wang Wenbin ya ce, Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen sassauta yanayin jin kai na kasar Ukraine. (Zainab)