Ana fargabar mutanen da dama sun makake wasu kuma sun mutu yayin da wani bene mai hawa daya ya ruguje a daidai lokacin da ake yin ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren Laraba a Abuja.
Ginin yana kan titin Legas da ke unguwar Garki a gundumar Garki II a Abuja.
Wani ganau mai suna Tanko Dabo, wanda ke wajen bayan faruwar lamarin, ya ce ginin na dauke da dakunan kwana da dama, yayin da kasan ginin ke zagaye da shaguna.
Ya ce ginin ya ruguje ne a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda aka fara da misalin karfe 11:50 na daren Laraba.
“An yi ta kuka a ko’ina bayan ginin ya ruguje. Ana hasashen Mutane da dama sun mutu yayin da ginin ya rufta baki daya.”